Thor ya karanci manyan amalankun dawakain, ya kuma fahimci cewa baza su dauki sabobbin dauka da yawa ba. Babban masarauta ne, kuma zasu ziyarci garuruwa da yawa. Ya hadiye yawu, yana mai gane cewa yiyuwan samun shigansa dan kadan ne ba Kaman yanda shi ya dauka da ba. Sai shi ya doke duka shauran yara maza – mafi yawansu kuwa gugaggun mafadata – tare da yan’uwansa uku. Wannan tasa jikinsa ya mutu.
Da mayakin ya fara takawa da dadaya a cikin yanayin shuru sai numfashin Thor na neman ya dauke, ya fara daga karshen angwa, yana zagawa a hankali. Thor ya san duka shauran yara mazan, sani na musamman. Ya san wadansunsu aboye basua son a daukesu, dukda cewa iyalensu nason su rabu dasu. Suna soron; bazasu kasance mayaka masu kuzari ba.
Thor nata fama da rashin ji da kai. Yanajin cewa shi ya cancanci a zabe shi Kaman kowane a cikinsu. Kasancewa yan’uwansa sun fishi shekaru da girman jiki da karfi baya nufin ya rasa damarsa na ya tsaya a kuma zabe shi. Yana ta jin kiyyaya wa mahaifinsa, ya kuma kusan fita daga haiyacinsa a yayinda mayakin ya kusanto.
Mayakin ya tsaya, a karo na farko, a gaban yan’uwansa. Ya kallesu sama da kasa, yayi Kaman sun yakeshi. Ya mika hanu, ya kamo daya daga cikin zabirunsu, ya fincikoshi, Kaman yana son ya gwada karfinsa.
Sai yayi murmushi.
“Baka taba amfani da takwafin ka a yaki ba, ko ka taba?” ya tambayi Drake.
Thor yaga Drake yana bari a karo na farko a rayuwansa. Drake ya hadiye yawu.
“Babu, maigidana. Amma nayi amfani dashi sau dayawa a cikin muraja’a, kuma ina fatan na—“
“A muraja’a!”
Mayakin ya fashe da dariya sai ya juya zuwaga shauran mayakan, wayanda suma suka shiga, dariya a gaban Drake.
Drake ya zama jazur da kunya. Wannan ya kasance karo na farko da Thor zai fara ganin Drake ya ji kunya. – abinda aka saba gani, shi yake kunyata wadansu.
“To dai zan tabattar na gaya wa makiyanmu su ji tsoronka – kai mai amfani da takwfinka a muraja’a!”
Taron mayakan sun sake fashewa da dariya.
Sai mayakin ya juyo zuwaga shauran yan’uwan Thor.
“Yara maza uku daga tushi daya,” injishi, yana shafan tushin gemanyan kan habansa. “Da zasu iya amfani. Dukanku agine da girma mai kyau. Duk da ba a gwadaku ba. Zaku bukaci koyaswa sosai idon har zaku samu cancanta.”
Sai ya dan saurara.
“Ina gani zamu iya neman gurbi.”
Yayi nuni dakai zuwaga bayan amalanken.
“Ku hau, kuma kuyi da sauri. Kafin na canja ra’ayi na.”
Duka yan’uwan Thor uku sun ruga zuwa amalanken, suna murmushi. Thor ya gano mahaifinsa, shima yana murmushi.
Amma bai ji dadi ba ayayin da yake kallon tafiyansu.
Mayakin ya juya ya kama tafiya gida na gaba. A nan Thor ya gagara kara hakuri.
“Yallabai!” Thor yayi kira da karfi.
Mahaifinsa ya juyo sai ya ware masa idanu, amma Thor ya wuce matsayin ya damu.
Mayakin ya saya, bayansa a juye zuwa gareshi, sai ya juyo a hankali.
Thor ya dauki taku biyu zuwa gaba, zuciyarsa tana bugawa, sai ya turo kirjinsa waje gwargwadon iyawansa.
“Baka duba lamarina ba, yallabai,” yace.
Mayakin, da mamaki, ya kalli Thor sama da kasa kaman abin wasa.
“Ashe ban duba ba?” ya tambaya sai ya fashe da dariya.
Yan bayansa ma sun fashe da dariya, suma. Amma Thor bai ko damu ba. Wannan ne lokacinsa. Ko yanzu ne kokuma babu har abada.
“Ina son na shiga rundunan!” Thor yace.
Mayakin ya taka zuwaga Thor.
“Yanzu kana son haka?”
Yayi kama da abin yana bashi dariya.
“Kuma ka kai shekaranka na goma sha hudu?”
“Na kai, yallabai. Sati biyu da suka gabata.”
“Sati biyu da suka gabata!”
Mayakin ya kyalkyale da dariya, hakama mutanen da suke bayansu.
“A cikin wannan yanayin, makiyan mu zasu tabattu a kan bari daga sun ganka.”
Thor yaji shi yana konuwa da rasin ji dakai. Dole yayi wani abu. Ba zai bari yakare haka ba. Mayakin ya juya don ya tafi – amma Thor ba zai iya barin hakan ya faru ba.
Thor yayi taku zuwa gaba sai yayi ihu: “Yallabai! Kana son kayi kuskure!”
Sanda kowa a taruwan jama’a ya ja numfashin tsoro, yayinda mayakin yasake sayawa ya juyo a hankali.
Yanzu sai ya matsa goshinsa a cikin fushi.
“Wawan yaro,” mahaifinsa yace, ya cafke Thor a kafada, “koma ciki!”
“Bazanje ba!” Thor yayi ihu, ya girgiza ya kubuta daga cafkewan mahaifinsa.
Mayakin yatako zuwa gaba ya nufi Thor, sai mahaifinsa yaja dabaya.
“Kasan horon da ake yiwa wanda ya zagi dan Silver?” mayakin ya tambaya da barazana.
Zuciyan Thor nata daka, amma ya san bazai ja da baya a yanzu ba.
“Dan Allah ka yafe masa, yallabai,” mahaifinsa yace. “Shi karamin yaro ne kuma----”
“Ba dakai nake Magana ba,” mayakin yace. Da wani kallon raini, ya tilasta wa mahaifin Thor ya juya ya koma.
Mayakin ya juyo zuwaga Thor.
“Bani ansa!” yace.
Thor ya hadiye yawu, ya gagara Magana. Ba haka yaga kasancewan lamarin a kwakwalwansa ba.
“Zagin dan Silver na daidai da zagin sarki da kansa ne,” Thor yace da ladabi, yana mayar da abin da ya koya daga tunani.
“Haka,” inji mayakin. “Wannan na nufin zan iya maka bulala arba’in in naga dama.”
“Bana nufin in zageka, yallabai,” Thor yace. Inason a dauke nine kawai. Kayi hakuri. Nayita mafarkin wannan duk tsawon rayuwana. Kayi hakuri. Ka barni na samu shiga.
Mayakin ya kalleshi, sai a hankali, yanayinsa ya yiwo laushi. Bayan dan lokaci mai tsawo, sai ya girgiza kai.
“Kai karami ne, yaro. Kana da zuciyan maza. Amma ba a shirye kake ba. Ka dawo ka samemu in an yayeka.”
Da waanan, sai ya juya ya ruga, bama kallon shauran yara mazan. Ya hau dokinsa a gagauce.
Thor, rai a bace, ya kalli tayarwan tawagan; Kaman yadda suka iso da sauri, suka tafi.
Abu na karshe da Thor yagani shine yan’uwansa, azaune a bayan rumfan amalanken karshe, suna kallonsa, da rashin aminci, suna masa dariya. Ana tafiya dasu a gaban idonsa, nesa daganan, zuwaga rayuwa mafi inganci.
Daga cikin zuciyarsa, Thor yaji Kaman yamutu.
Da hayaniyan da ya kewaya shi ya kare a hankali, duk mutanen kauyen su sun kokkoma gidajensu.
“Kasan irin wawancinda kanuna, wawan yaro?’ mahaifinsa ya haura, ya kuma cafke kafadunsa. “Kasan da zaka iya bata wa yan’uwanka sa’ansu da zarafinsu?”
Thor ya ture hannayen mahaifinsa daga jikinsa da haushi, sai mahaifin ya miko hanu ya mari fuskansa da bayan hanu.
Thor ya ji zafin abin ya mayar da hararo ga mahaifinsa. Wani bangarensa, a karo na farko, yaso ya rama marin da mahaifin ya masa. Amma ya kama kansa.
“Je ka dawo da garken tumakina. Yanzu! Kuma in ka dawo, karka sa ran zan ciyar da kai. Za ka rasa abincin daren yau, sai kayi tunani a kan abinda ka aikata.”
“Watakila bazan ma dawo ba gaba daya!” Thor na ihu yana juyawa don ya tafi, ya bar gida, ya nufi su tudun bayan gari.
“Thor!” mahaifinsa ya kira da karfi. Yan kalilan din kauyawan da suka rage a kan hanya sun saya suna kallo.
Thor ya fara shi ba gudu ba shi kuma ba tafiya ba, sai ya fara gudu, yanason ya nisanci wannan gurin gwargwadon abinda ya samu. Baima san shi ya fara kuka ba, hawaye sun mamaye fuskarsa, yayin da duk mafarkun da ya taba rike wa a zuciyarsa suka cikaro da mummunan mutuwa.
SURA NA BIYU
Thor yayita yawo a cikin daji na sa’oi, cike da fushi, kafin daga karshe ya zabi wata yar tudu ya zauna, hannayensa a nade a kan kafafuwansa, yana kallon sararin Allah. Ya kalli bacewan amalankun, yayita kallon kuranda suka tayar na wasu sa’oi bayan su sun bace.
Bazasu sake kawo wata ziyara ba. Yanzu ya kamu da kaddaran zaman kauyen nan na shekaru kenan, yana jiran wata zarafin – idon ma sun dawo kenan. In kuma mahaifinsa ma ya yarda kenan. Yanzu zai zama shi da mahaifinsa, su kadai a gida, kuma tabattace mahaifinsa zai huce haushinsa a kanshi. Zai cigaba da kasancewa bawan mahafinsa, shekaru zasu yita tafiya, sai shima ya karasa rayuwansa Kaman nashi, a makale da dan karamin rayuwa, na leburanci – alhali yan’uwansa sunsamu yabo da sanuwa. Jininsa nata tafasa da rashin ji dakai a kan lamarin duka. Ba wannan rayuwan yakeso ba. Kuma shi ya san da haka.
Thor yacigaba da wasa kwakwalwa ko akwai abinda shi zai iya yi, ko ta wani hanya domin ya juya lamarin. Amma babu komai. Kaman haka kaddara da rayuwa ya rubuta masa zai kasance.